Supetocin IAEA sun isa Iran. | Labarai | DW | 10.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Supetocin IAEA sun isa Iran.

Supetocin hukumar kula da kare yaduwara makaman nukiliya ta kasa da kasa sun isa kasar Iran domin duba tashar nukiliya ta dake Natanz .

Kanfanin dillancin labaru na Fars ya sanarda da cewa wannan shine karo na biyu da supetocin hukumar suka kai ziyara Iran cikin wannan shekara.

Wannan ziyara kuwa tazo ne kwana guda bayab shugaba Ahmedinajad ya sanarda shiga wani sabon shafi a shirin nukiliya na kasar.