Sunayen gwarzayen FIFA na bana
FIFA ta sanar da sunayen karshe na gwanayen da za'a mikawa kyautar bajinta, ciki akwai 'yan wasa da masu horaswa. Za'a sanar da wadanda suka yi nasara ran tara ga watan Junairun badi, ga wasu da ake zaton su kai labari
Antoine Griezmann
Dan wasan gaba na Faransa da Atletico Madrid ya shiga jerin bayan kokarin da ya yi a bana, abin da ya bashi damar kaiwa ga Champions League da EURO 2016. Ko da yake dukkan wasannin ba a ci su ba, biyo dokewar da aka yi wa Griezmann a wasannin karshe, Bafaranshen ya yi kokuwa kan kwallaye 40 a kaka'ar wasa ta 2015/16.
Cristiano Ronaldo
Real Madrid da Portugal mutumin da ko yaushe ke gaba a yawan kwallaye, ya hanawa Griezmann nasara a gasannin UEFA da Champions League da EURO 2016. Ronaldo ya samu kyautar Los Merengues, kyauta ta 11 a Turai bayan zura kwallo a Penalty a karawarsu da Atletico Madrid kafin ya zame captain din Portugal, abinda ya kai su ga nasarori da yawa
Lionel Messi
Dan Ajantina ya samu kyautar La Liga sau takwas da kuma Copa del Rey sau hudu, inda yake bugawa Barcelona a 2016. Ya kuma yi captain Ajantina a gasar Copa America, inda kasar Chile ta doke su a wasan karahe da bugun penalty. Messi ya kare gasar a matsayin wanda ya fi taimakawa aci da kuma na biyu a yawan zura kwallaye.
Silvia Neid
Tsohuwar mai horas da 'yan matan kwallon kafan Jamus ta lashe zinari a gasar Olympic na bana a Rio. Kuciyar ta taba lashe gasar gwallon kafa na duniya a 2007 kana sau biyu tana zama zakaran kuciyoyin mata na duniya. Neid ta kammala horaswa na tsawon shekaru 11 tana horas da 'yan matan DFB bisa nasarori, a lokacin suka doke Sweden 2-1 a filin wasa Maracana kafin ta yi ritaya.
Jill Ellis
Ellis ta lashe kyautar FIFA ta 2015 a lokacin da taimaka ta kai kungiyatr kwallon kafan matan Amirka a 2016, 'yan wasanta ba su lashe gasar ta Olympic ba, amma sun yi nasara a wasannin 22 daga 25 da suka buga, sun yi kunne doki a wasannin uku ciki har buga penality da Sweden a Brazil), sun zura kwallaye 110
Melanie Behringer
Behringer ta yi ritaya daga wasa da lashe zinari a Rio Olympic 2016. Inda Bajamusar a aka rubta sunanta a fulunan hana salla 120, ita ce ta fi kowa zura kwallaye a gasar ciki har da biyar masu mahimmanci ga Jamus. Ta kuma tabbatar mahimmancin club din ta, wajen tallafawa Bayern Munich lashe gasar championship
Marta
Yar kasar Burazil ta na a matsayin mace da tafi iya buga kwallo a duniya. Marta an zabe ta matsayin wace tafi dacewa a kyauta mafi daraja sau 12 cikin 13 da aka taba yi, kuma ta samu kambun gwarzuwa har sau biyar a jere. Ko da yake 'yar shekaru 30 da haifuwa ta gaza samun lambar zinari a gasar Olympic wanda aka yi a Brazil kasar haifuwarta, ta ci gaba da zama mace mafi fice a fagen wasa
Zinedine Zidane
'Zizou' ya ci wa Real Madrid's gasar UEFA Champions League na tara a farkon shekararsa ta horas da kungiyar, ga wannan fitaccen kan kwallo a 2002. A 2016 Bafranshen ya dawo inda ya ci wa kulob din gasar European Cup. Zidane ya samu karin kaimi a bugawar karshe da Atletico Madrid. A nanne Zidane mutum na farko da ya lashe gasar a matsayin dan wasa da kuma a lokacin yana mai horaswa.
Fernando Santos
Haifaffen Lisbon ya yi tarihi bisa nasarar Portugal a wasanni masu karfi na EURO 2016. Santos ya yi aiki da kwarewar Cristiano Ronaldo, inda kusan ya dogara da captain din a tsawon gasar. Har ila yau, Santos ya yi dabarun tare kasar Faransa ba tare da taimakon Ronaldo ba a wasan karshe wanda suka lashe da 1-0 bayan karin lokaci
Claudio Ranieri
Kucin Italiya shi ya tsara nasarar ba zata da Leicester City's suka yi a Premier League na 2016. Ranieri, ya ceto Foxes a 2015 kolub da ke dab da komawa rukunin baya. Amma Ranieri ya nuna dabarunsa inda ya kai ga kulob din ya yi nasarar tarihi a shekaru 132.