Sumame kan masu jibi da ta′addanci a Jamus | Siyasa | DW | 15.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sumame kan masu jibi da ta'addanci a Jamus

Jami'an tsaro sun gudanar da bincike a wasu jihohin kasar da dama da nufin bankado wadanda ke da hannu wajen tallafa wa 'yan kungiyar nan ta IS da ke rajin girka daular Isama.

Baya ga wannan sumamen, a daya hannun kuma hukumomin kasar ta Jamus sun sanar da haramta ayyukan wata kungiyya ta 'yan Salafiyya da ta yi suna wajen rarraba Alku'arni mai tsarki a wasu manyan birnen kasar. Izuwa wayewar garin Talata (15.11.2016) an kai sumame a masallatai da gidaje da ofisoshi kimanin 190 a birane 60, ciki kuwa har da Berlin wanda ke zaman babban birnin kasar ta Jamus. Galibin wuraren da 'yan sanda suka gudanar da wannan binciken na mambobin Salafiyya a kasar wadanda ake tunanin a asirce suna aiki tare da 'yan IS ne.

Yayin wannan bincike dai 'yan sanda sun ce sun yi awon gaba da wasu takardu da dama daga ofosisoshin 'yan wannan kungiyar da ake zargin ta na da alaka da kungiyar nan ta IS da ke jagorantar ayyukan ta'addanci a duniya. Hukumomi a Jamus suka ce jami'an tsaronsu sun yi wannan aiki ne da nufin ganin ayyukan ta'addanci ba su samu gindin zama a kasar ba, musamman ma da yake makotanta wato Beljiyam da Faransa sun fuskanci tada kayar baya ta 'yan kungiyar IS. Thomas de Maiziere da ke zaman ministan harkokin cikin gida na Tarayyar Jamus ya ce :

"Ko kusa ba ma son ganin ayyukan ta'addanci a nan Jamus, kuma ba ma son ganin an samu wasu da za su tallata wannan ala'amari. Kuma ba ma son ganin an cusawa mutane tsattauran ra'ayi na addini, kana ba ma son ganin an yi amfani da kasar wajen kai harkokin ta'addanci zuwa wasu kasashe. Wannan aiki da aka yi 'yar manuniya ce ta shaukin da muke da shi na ganin mun kare 'yancin da kasarmu ke da shi da ma irin tsarin da muka ginu a kai".

To baya ga batu na bincike da kuma dakile wanzuwar ayyukan masu tsaurin kishin addini kamar 'yan IS, a share guda ma'aikatar harkokin cikin gidan Jamus, ta kuma haramta ayyukan kungiyar nan da ke rarraba Alkur'ani a kasar wadda ake wa lababi da ''True Religion'' kuma wannan haramci da gwamnati ta yi ya fara aiki ne daga safiyar wannan Talatar (15.11.2016). Kamar yadda ministan cikin gidan kasar ya yi karin haske:

"A matsayina na ministan cikin gidan Jamus na haramta ayyukan wannan kungiya ta ''True Religion'' domin kuwa kungiyar na hada kan 'yan ta'adda da ke fadin kasar, inda suke fakewa da bunkasa addinin Islama ta hanyar rabon Alkur'arni mai tsarki wanda aka yi wa tarjama.

Sai dai a daura da wannan, hukumomi a Berlin sun ce wannan mataki da suka dauka bashi da nasaba da yunkuri na hana gudanar da addinin Musulunci a kasar da ma ciyar da shi gaba, domin kuwa kowa na da yanci na yin addinin da ya ga dama kuma ma Musulunci addini ne da ya kafu kuma ya yi rassa a kasar, don haka ba su da wata manufa mummuna gare shi.

Wannan lamari dai na wakana ne daidai lokacin da shugaban kungiyar ta ''True Religion'' da aka haramta ayyukanta, wato Ibrahim Abou-Nagie wanda haifaffen Falasdinu ne, ya isa kasar Malesiya da nufin kaddamar da reshen wannan kungiya tasu a kasar da ma aikinta na raba littafi mai tsarki a kasar. Ya zuwa yanzu dai 'yan wannan kungiya ta ''True Religion'' ba su kai ga cewa komai ba dangane da wannan haramci da aka yi musu.

Sauti da bidiyo akan labarin