Sulhuta rikicin Dafur ya ci tura | Labarai | DW | 05.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sulhuta rikicin Dafur ya ci tura

Tattaunawar shirin samar da zaman lafiya a lardin Dafur wanda ya gudana a birnin tarayyar Nigeria Abuja yaci tura bayan da biyu daga cikin ƙungiyoyi uku na yan tawayen suka yi fatali da daftarin yarjejeniyar da aka tsara. ƙungiyar yan tawaye ta JEM da kuma takwarar ta SLA sun ce ba za su sanya hannu a kan yarjejeniyar ba har sai an yiwa daftarin wasu yan gyare gyare. A tsakar daren jiya ne dai waádin da ƙungiyar gamaiyar Afrika wadda ke shiga tsakanin domin sasanta rikicin ya ƙare wanda kuma ke zama karo na uku da aka bada wannan waádi a yan kwanakin da suka gabata, a kokarin kawo ƙarshen rikicin da ya haddasa ɓarkewar taroma a yankin na Dafur. A na ta ɓangaren gwamnatin Sudan ta amince da yarjejeniyar sulhun amma ƙungiyoyin yan tawayen sun ƙi bada hadin kai. ƙungiyar gamaiyar Afrika wadda ke kaiwa da komowa don kawo ƙarshen rikicin ta ce ba zata sake buɗe wata tattaunawa a game da daftarin da aka riga aka cimma ba. An dai shafe tsawon shekaru biyu ana gudanar da shawarwari a birnin tarayyar Nigeria Abuja domin gano bakin zaren warware rikicin na yammacin Sudan.