1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sulhunta rikicin gabas ta tsakiya

August 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bulr

Muƙaddashin sakatare a majalisar ɗinkin duniya a kan alámuran siyasa Alhaji Ibrahim Gambari ya yi kiran gudanar da wani sabon yunkuri domin warware rikicin yankin gabas ta tsakiya. Alhaji Ibrahim Gambari wanda ya baiyana cewa shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya ya shiga wani hali mawuyaci, ya yi kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa su himmatu wajen samar da sahihan matakai domin warware rikicin Israila da Palasdinawa da Syria da kuma Lebanon. Gambari ya shaidawa kwamitin sulhun na Majalisar ɗinkin duniya cewa rikicin yankin na gabas ta tsakiya na buƙatar kwamitin ya samar da matakai ingantattu domin sasanta rikicin don samun dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya. Kiran na Ibrahim Gambari ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar ƙasashen larabawa ke shirin gabatar da jadawalin shawarwari ga Majalisar ɗinkin duniyar domin kawo karshen rikicin dake tsakanin Larabawa da Israila ta hanyar kafa yantacciyar ƙasar Palasdinawa da warware rikicin tsaunin Golan na Syria da kuma ƙarfafa samun zaman lafiya a tsakanin Israila da Lebanon.