1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sulhu tsakanin shugabanin kungiyar Tawayen Darfur

Yahouza SadissouNovember 28, 2005

Shugabanin kungiyar tawayen SLA ta yankin Darfur sun sulhunta juna, kamin shawarwarin Abuja

https://p.dw.com/p/Bu3v

Bangarori 2 masu gaba da juna, a kungiyar tayawen yankin Darfur na kasar Sudan, sun bayyana dimke baraka, domin fuskantar sabin shawarwarin zaman lahia zagaye na 7, da za a koma gobe idanAllah ya kai mu a birnin Abuja na tarayya Nigeria.

Sabanin ra´ayoyi da su ka kunno kai, tsakanin kungiyar tawayen SLA, na daga matsalolin da su ka dabaibaye wannan shawarwari, da su aka ci su ka cu cenyewa.

Saidai kamin ma a ke zauna tebrin tantanawar, masharahanta na nuni da cewa, za a koma gidan jiya noman goje, mussamman ta la´akari da matsalolin jagoranci tsakanin shugabanin yan tawayen, da hauhawar tashe tashen hankulla, a yankin Darfur , sannan ga ita kanta gwamnatin Sudan, bisa dukan alamu ba da zucciyya daya, ta ke wannan tantanawa ba, sai kuma uwa uba, su wanda su ke barin wuta a fagen daga,na bangarorin 2 ba su matsu ba, su ajje makamai.

A karshen makon da ya wuce, shugabanin tawayen 2, masu bukatar jagorancin kungiyar, sun halarci taron sulhu a birnin N´Djamena na kasar Tchadi, bisa gayyatar kasashe masu shiga tsakani, da su ka hada da Tchadi Lybia, Erythrea da kuma kungiyar Taraya Afrika.

Kakakin kungiyar AU, Salim Ahmed Salim ,ya bayyana cewa Minni Arcua ,da Abdelwaheed Mohamed dukkan su biyun, sun amince su sassanta da junan su, domin samun mafita a wannan takkadama,za su kuma halarci taron na Abuja da murya daya.

A yanzu haka, a cewar Ahemd Salim sun issa birnin na Abuja.

A taron kwanakin baya, da ya watse baran baram, daya daga madugun yan tawayen, wato Minnawi , sarai kauracewa yayi , to amma a wannan karo yayi amana, ya bada hadin kai.

Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan ,yayi kira ga gwamnatin Sudan da yan tawaye, da su yi iya kokarin su, domin a cimma nasara a wannan karo.

A satin da ya wuce itama kungiyar taraya Afrika, ta yi barazanar saka takunkumi ga shugabanin yan tawayen, muddun su ka ci gaba, da mayyar da hannu agogo baya, a fadi ka tashin da a ke na warware wannan rikici.

A wani labarin kuma da ya shafi Tchadi da Sudan, jam´iyun siyasa masu rike da ragamar mulki a wannan kasashe, sun hiddo sanarwar hadin gwiwa ,inda su ka bayyana bukatar su, ta ganin an samu fahintar juna tsakanin kasashen 2.

A baya bayan nan, an yawaita fuskantar sabani, tsakanin fadar gwamnatin Khartum da ta N Djamena.

ShugabanEl bashir ya tuhumi rundunar tsaron Tchadi, da shiga iyakar Sudan, da kuma shawagi a sararain samaniyar ta ba tare da izini, a yayin da Tchadi, ke zargin Sudan, da bada mafaka da gungun sojojin ta da su ka tsere , wanda kuma ke ci gaba da kai hare-hare ga dakarun gwamnatin Tchadi.

Sanarwar hadin gwiwar da jam`iyun 2, su ka fido ta tanadi hussa´ao´i, da dubaru na warware rashin jituwa cikin ruwan sanhi, ba tare da tada hankulla ba.