1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sukan manufofin Turai akan Afrika

Zainab MohammedDecember 11, 2007

Kungiyoyi masu zaman kansu na sukan yadda turai kewa Afrika

https://p.dw.com/p/CaNM
Commissionan kasuwanci na turai, Peter Mandelson.Hoto: AP

Duk dacewar ƙasashen Turai basu da wani nisa daga na Africa,bisa dukkan alamu za a iya kwatanta su da kasancewa tafiya daga nahiya zuwa wata,musamman bisa la’akari da giɓin dake tsakanin na turai ɗin dake da bunkasar tattalin arziki,a hannu guda kuma takawarorin su na Afrika dake fama da matsaloli na ƙulla dangantakar kasuwacin dasu.

Duk dacewar kimanin ƙasashen turai dana Africa 70 suka samu halartan taron birnin Lisbon daya gudana a ƙarshen mako,inda akayi kokarin ɓoye giɓin dake tsakanin ɓangarorin biyu musamman dangantakar zama kafaɗa da kafaɗ bayan mulkin mallaka,babu alamun an cimma dalilan da suka haifar da gudanar da wannan taro na yini biyu.

Shugabar Gwamnatin Jamus dai ta soki ƙasashen Africa adangane da halin da ake ciki a Zimbabwe,inda shugabannin turai ɗin ke zargin Robert Mugabe da musgunawa Abokan adawa tare kara durkusar da tattalin arzikin ta.

Wakilan kasashen turan dai sun tabbatarwa da takwarorinsu na Africa cewar,zasu ci gajiyar sabuwar yarjejeniya mai sassauci kan harkokin kasuwanci ,wadda turai ta nacewa rattaba hannu akai kafin cikan wa’adin kungiyar ciniki ta duniya a ranar 31 ga watan Disamban da muke ciki.

Sai mafi yawa daga cikin shugabannin ƙasashen Africa akarkashin jagorancin shugaban Senegal Abdoulaye Wade,sun yi adawa da sabuwar yarjejeniyar dangantakar tattalin na turai,ko kuma wani shiri a madadinsa,inda suka ce hakan na bayyana wariya ne a fili.

Shugaba Wade yayi gargaɗin cewar irin tsarin tafiyar hawainiya da turai keyi,zai haifar mata da barazanar koma baya,bisa la’akari da yadda kasashen Sin da India k erige rigen zuba jarinsu a Africa.

Wade dake zama shugaban Africa ɗaya tak da yayi hira da manema labaru,ya bayyana adawarsa adangane da tattaunawar cimma yarjejeniyar kasuwanc8i tsakanin nahiyoyin biyu.

Ƙungiyoyin kare hakkin jamma’a ,da masu yaki da talauci a duniya dai na cigaba da sukan yaddad ɓangarorin biyu suka yiwa wannan dama da suka samu,rikon sakainar kashi wajen tallafawa milliyoyin mutane dake fama da ƙangin talauci a nahiyar Africa,tare da magance mafia muni daga cikin irin rigingimu da nahiyar ke fama dasu,kamar na lardin Darfur.

To sai shugaban ciniki na turai yayi watsi da sakamakon taron dake nunar dacewa shugabannin Africa sun cimma sabuwar yarjejeniya da turai,inda ya lashi takobin cimma waadin karshen shekara,kafin a sanya haraji.

Peter Mandelson yace kalaman suka daga shugabannin Senegal da Africa ta kudu a wajen taron na karshen mako ya nunar dacewa,turai na samun cigaba adangane da cimma hadin kai na tattali da kasashen na Africa.