1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suka kan zaɓen Burma

November 9, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya ta koka kan zaɓen da aka yi a ƙasar Burma ko Myanmar

https://p.dw.com/p/Q2fO
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moonHoto: AP

Babban sakataren MDD Ban ki-moon ya soki zaɓe da aka yi a ƙasar Buma, wanda a hukumance ake kira Myanmar. Babban sakataren majalisar wanda ya yi magana ta bakin kakakinsa, ya buƙaci da a saki fursunonin siyasa da aka ɗaure, ciki har da madugar 'yan adawa Aung Sang Suu Kyi. Sojojin dake mulkin ƙasar dai sun yi iƙirarin lashe kashi 80 cikin ɗari na kujerun da aka zaɓa. A halin da ake ciki kuwa ana ci gaba da faɗa tsakanin 'yan tawayen ƙasar da dakarun gwamnatin ta Buma a kan iyakar su da ƙasar Thailand. Kamar yadda mazauna inda ake faɗan suka bayyana, suna jin tashin bindigogi. Tun bayan sanar da sakamakon zaɓe ne dai faɗa ta kaure tsakanin ɓangarorin biyu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu