Sudan tayi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya akan Darfur | Labarai | DW | 13.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan tayi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya akan Darfur

Kasar Sudan tayi watsi da rahoton da MDD ta fitar inda ta zargi gwamnatin Sudan da haddasawa tare da aikata laifukan yaki da take hakkin bil adama a yankin Darfur.

Ministan sharia na Sudan Muhammad Ali Elmardi ya fadawa taron majalisar kula da kare hakkin bil adama ta MDD a Geneva cewa ba dukkanin membobin majalisar 5 bane suka gudanar da wannan bincike saboda haka a cewarsa rahoton bashi da tushe.

Kana yayi kira ga majalisar da tayi watsi da abinda rahoton ya kunsa.

MDD ta kiyasta cewa akalla mutane 200,000 suka halaka wasu miliyan 2.5 aka tilasatawa barin gidajensu tun lokacinda rikicin Darfur ya barke shekaru 4 da suka shige.