Sudan ta yiwa Jamián Amurka Talala | Labarai | DW | 25.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta yiwa Jamián Amurka Talala

Shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir ya sanya dokar taƙaita zurga zurgar jamián Amurka a cikin ƙasar Sudan ya zuwa daírar kilomita 25 daga birnin Khartoum. Yana mai ƙarfafa dokar da cewa haka ita ma Amurka ta yiwa jamián ƙasar Sudan a New York, a lokacin taron Majalisar ɗinkin duniya wanda ya gudana a makon da ya gabata. Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar gamaiyar Afrika ke shirin tura ƙarin dakarun soji zuwa Sudan domin ƙarfafa waádin lokaci da aka karawa sojin ta dake aikin kiyaye zaman lafiya a lardin Dafur mai fama da rikici. Fadar Khartoum na cigaba da turjiya a game da buƙatar tura sojin ƙasa da ƙasa su kimanin 20,000 ƙarkashin inuwar Majalisar ɗinkin duniya zuwa Dafur inda aka yi ƙiyasin mutane 200,000 sun rasa rayukan su bayan da tarzoma ta ɓarke a yankin a shekarar 2003.