1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta umurci Jan Pronk ya gama yanasa-yanasa ya bar ƙasar.

October 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buey

Ƙasar Sudan ta umurci wakilin MDD da ke birnin Khartum, Jan Pronk, ya gama ya nashi yanashi, ya fita daga ƙasar, nan da kwanaki 3 masu zuwa.

Khartum, ta ɗauki wannan mataki, domin maida martani ga hurunci da wakilin na MDD yayi ranar juma´a da ta wuce inda ya ce yan tawayen Darfur, sun fattataki dakarun gwamnatin a wata taho mu gama da su ka yi.

A ci gaba kuma da neman hanyoyin waware rikicin yankin,Ƙasar Masar, ta bada wata sabuwar shawara.

Ministan harakokin wajen ƙasar, Ahmed Abdoul Gheit, ya bayyana wannan shawara, bayan ganawar da yayi da saban wakilin Amurika a Sudan Andrew Natsios.

Masar ta yi kira ga MDD, ta bada issasun kuɗaɗe ga Taraya Afrika,domin ta ci gaba da ayyukan tsaro a yankin Darfur.

Wannan mataki zai kawo ƙarshen taƙadama tsakanin hukumomin Khartum, da Majalisar Ɗinkin Dunia, bayan da shugaba Omar Hassan El-Bashir, ya yi tsawuwar gwamen jaki, a kan batun ƙin amincewa da karɓar tawagar sojojin Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.