1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta musanta yiwa kasashen Afirka da na Larabawa barazana

October 7, 2006
https://p.dw.com/p/Buh9
Gwamnatin Sudan ta musanta cewa ta gargadi kasashen Afirka da na Larabawa da ka da su tura dakarunsu zuwa lardin Darfur. Wata wasika da tawagar Sudan a MDD ta aike da ita ta ce zata dauki duk wani karokaron soji da za´a ba wa rundunar da MDD ke shirin girkewa a Darfur, a matsayin nuna mata adawa. Ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol ya ce wasikar ba ta nuna matsayin gwamnatin sa ba. MDD na son girke dakaru kimanin dubu 20 don kawo karshen rikicin lardin na Darfur to amma Sudan na zargin cewa kasashen yamma na son su yi amfani da sojojin don mamaye kasar. A halin da ake ciki Amirka ta yi kira ga MDD da ta gudanar da taron gaggawa a kan wannan wasika wadda ta bayyana ta da cewa wani kalulable ne kai tsaye ga kwamitin sulhu.