Sudan ta Kudu: Manyan sojoji na juya wa Shugaba Salva Kiir baya | Labarai | DW | 18.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta Kudu: Manyan sojoji na juya wa Shugaba Salva Kiir baya

An sake samun babban jami'in sojan Sudan ta Kudu da ya ajiye aiki a wani mataki na kokarin mayar da Salva Kiir saniyar ware.

Shugaban kotun soja ta Sudan ta Kudu Kanar Khalid Ono Loki ya ajiye aiki, inda ya ce shish-shigi daga manyan jami'ai sun gurgunta biyayya tsakanin sojojin kasar, wadanda ake zargi da fyade da kisan gilla sakamakaon rikicin da kasar ta samu kanta a ciki.

Kanar Khalid Ono Loki ya zama babban jami'in gwamnati na uku da ya yi murabus cikin mako guda, abin da ake gani zai kara rashin kima da gwamnatin Shugaba Salva Kiir mai fuskantar yakin basasa tun shekara ta 2013, lokacin da shugaban ya sallami mataimakinsa Riek Machar daga bakin aiki, lamarin da ya zama na kabilanci tsakanin 'yan bangaren Dinka na Shugaba Kiir da kuma 'yan Nuer na Machar.

Majalisar Dinkin Duniya ta tattara shaidu na daruruwan fyade da ake zargin sojojin gwamnati, kana 'yan gwagwarmaya suna zargin wasu 'yan tawaye da cin zarafin mutane. Akwai kimanin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu 15 a kasar ta Sudan ta Kudu, wadanda ake suka saboda rashin shiga domin kare fararen hula.