1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta kori wakilan EU da na Kanada daga Khartum

August 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuDH

Ƙasar Sudan ta kori wakilan ƙungiyar taraya Turai, da na Kanada daga birnin Khartum, tare da zargin su, da shiga sharo ba shanu, a harakokin ta, na cikin gida.

Wakilin EU, Kent Degerfelt, ya mussanta zargin da ake masa, na yin katsa landan, a harakokin da ba su shafe shi ba, a ƙasar Sudan.

Ƙungiyar taraya turai ta bayyana rashin gamsuwa da wannan mataki na hukumomin Khatrum .

Haka zalika ƙasar Kanada, ta buƙaci Sudan ta bada haske a game da wannan mataki da ta ɗauka, wanda ka iya maiyar da hannun agogo baya, a hulɗoɗin ta, da ƙasashen ƙetare.

Cemma ma dai hulɗodi tsakanin Sudan da ƙasashen yammacin dunia, na ci gaba da ƙara gurbacewa.

A shekara da ta gabata, Sudan ta kori wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia, Jan Pronk, bayan yayi huruci, a game da rikici tsakanin dakarun gwamnatin Sudan, da yan tawayen yankin Darfur.