Sudan ta kori jakadun Canada da EU | Labarai | DW | 23.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta kori jakadun Canada da EU

Sudan ta kori babban jakadan kasar Canada da wakilin hukumar gudanarwa na kungiyar tarayyar turai, adangane da abunda ta bayyana da tsoma baki cikin harkokin cikin gida.Rahotannin kafofin yada labaru na kasar sun ruwaito cewa hukumomin Sudan din sun gurfanar da jakadun lokuta daban daban ne, kafin su mika musu takardun haramta musu cigaba da kasancewa acikin kasar.Har yanzu dai babu wanda yasan dalilin daya jagoranci koran wadannan jakatun turan guda biyu,koda yake kasashen yammaci na turai da dama sun sha sukan lamirin gwamnatin Khartum,adangane da irin rawa datake takawa cikin rigingimun lardin Darfur.