Sudan ta kara jaddada matakin ta na hawa kujerar naki | Labarai | DW | 20.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta kara jaddada matakin ta na hawa kujerar naki

Shugaba Omar Al Bashir na Sudan ya jaddada matakin cewa kasar sa ba zata yarda da zuwan dakarun sojin Mdd ba izuwa yankin Darfur.

A cewar shugaban na Sudan, a maimakon aikewa da dakarun sojin na Mdd, zai fi kyau kungiyyar hadin kann Africa ta kara yawan dakarun ta a yankin na Darfur.

Shugaba Al Bashir wanda a yanzu haka yake birnin New York don halartar taron kwamitin sulhu na kungiyyar Au, ya kuma soki kasashen dake kokarin gabatar da kuduri a gaban Mdd na aikewa da sojin kiyaye zaman lafiya izuwa kasar sa da cewa, suna yi ne da wata manufa.

Kalaman dai na Al Bashir da alama sun biyo bayan kiran da shugaba Bush na Amurka yayi ne ga Mdd da cewa akwai bukatar daukin ta a yankin na Darfur.