Sudan ta jaddada aniyarta a game da zuwan dakarun sojin Mdd | Labarai | DW | 28.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta jaddada aniyarta a game da zuwan dakarun sojin Mdd

Shugaban kasar Sudan , Omar Al Bashir yace kasar sa ba zata yarda da hadin giwar dakarun sojin kiyaye zaman lafiya ba, karkashin Mdd a yankin Darfur ba.

A cewar sugaban na Sudan, kasar sa zata amince ne kawai da tawagar kiyaye zaman lafiya a yankin na Darfur ne karkashin kulawar kungiyyar Au.

A maimakon zuwan tawagar sojin na Mdd izuwa yankin na Darfur, shugaban na Sudan yace kasar sa zata amince ne kawai da duk wani taimako na kudi ko kuma makamancin sa daga Mdd.

A can baya dai rahotanni sun rawaito mahukuntan na Sudan na nuna amincewa da dakarun sojin hadin gwiwar, karkashin kulawar Mdd, to amma daga baya sai suka hau kujerar naki.

Bayanai dai sun nunar da cewa sakataren Mdd, Mr Kofi Anan ne ya gabatar da tsarin tafiyar da dakarun sojin hadin giwar karkashin kulawar Mdd, a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya a yankin na Darfur.