1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta gurfanar da malama Gibbons gaban kotu

Yau ne aka gurfanar da malamar makarantar ‘yar Britaniya da ake zarginta da tunzure musulmi tare da cin zarafin addini da wulaƙanta tafarkin addinin musulunci gaban kotu a Sudan. Idan har an kamata da wannan laifi, Malama Gillian Gibbons mai shekaru 54 da haifuwa zata fuskanci hukuncin dauri a kurkuku, tare da tara ko kuma hukuncin bulala 40. Hukumomin Sudan sun cafke malamar bayan ta bari yara ‘yan makaranta sun sama wani ‘yar babin wasan yara suna Mohammed. Yanzu haka Britaniya tana neman izinin saduwa da jakadar Sudan a birnin London.