Sudan ta ce daidaiton da aka cim ma kan yankin Darfur bai ƙunshi girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin ba. | Labarai | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta ce daidaiton da aka cim ma kan yankin Darfur bai ƙunshi girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin ba.

Ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol, ya ƙarfafa cewa sakamakon da aka cim ma a taron Addis Ababa kan yankin Darfur, bai nuna cewa za a girke dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya su yi ta aikin haɗin gwiwa da takwarorinsu na Ƙungiyar Tarayyar Afirka ba. Ya ce yarjejeniyar, ta tanadi batun taimakon kayayyaki aiki ne da Majalisar Ɗinkin Duniyar za ta bai wa dakarun na Ƙungiyar AU. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai a wata fira da ya yi da gidan rediyon Omdurman, a karo na farko tun da aka ba da sanarwar cim ma yarjejeniyar jiya, ministan ya bayyana cewa, ba a yi wani batun girke dakarun haɗin gwiwa ba a taron na Addis Ababa. Abin da aka yarje a kansa shi ne girke dakarun Ƙungiyar Tarayyar Afirka tare da samun taimako daga Majalisar Dinkin Duniya.

A jiya ne dai babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar, Kofi Annan, ya ba da sanarwar cewa, an cim ma yarjejeniya wajen kafa wata rundunar dakarun kare zaman lafiya ta haɗin gwiwa tsakanin Ƙungiyar Haɗin Kan Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda za a girke a yankin na Darfur.