Sudan ta bada haɗin kai ga sakamakon taron Paris | Labarai | DW | 27.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta bada haɗin kai ga sakamakon taron Paris

Gwamnatin ƙasar Sudan, ta bada hadɗn kai ga shawarwarin da a ka tsaida, a taron Paris na ƙasar France , wanda ya tantana matsalolin yakin Darfur.

Idan dai ba manta ba ranar litinin da ta wuce wakilan ƙasashen Amurika, Taraya turai, Sin, Majalisar Dinkin Dunia, da kungiyar gamayyar Afrika,su ka shirya zaman taro na mussamnan, a birnin Paris, inda su ka amincewa da lunka ƙoƙari ta fannin yunƙunrin kawo ƙarshe tashe-tashen hankulla, da ke wakana a yankin Darfur.

Kakakkin ministan harakokin wajen Khartum Ali Sadeck ya tabbatar da cewa , gwamnati ta yi lale marhabin da ƙudurorin da taron na Paris ya cimma, duk da cewar da farko ta bayyana adawa da shi.

Sadeck ya ce yanzu,magana ta rage ga Majalisar Dikin Dunia, ta tanadi matakan aika rundunar haɗin gwiwar da ta ambata, tare da samar mata issasun kayan aiki.

Sannan gwamnatin Sudan za ta cika alƙawarin da ta ɗauka na bada haɗin kai.