Sudan ta amince da girke dakarun kungiyar AU da MDD a Darfur | Labarai | DW | 17.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta amince da girke dakarun kungiyar AU da MDD a Darfur

Sudan ta amince da a girke rundunar hadin guiwa ta sojojin kungiyar tarayyar Afirka da MDD a lardin Darfur mai fama da rikici dake yammacin kasar. Wakilan tawagar kwamitin sulhu suka tabbatar da haka bayan wata ganawa da suka yi da shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir a birnin Khartoum. Wakilan tawagar sun ce ba tare da ya gindaya wani sharadi ba, shugaba Bashir ya amince da girke rundunar da zata kunshi sojoji kimanin dubu 19. Tun a cikin makon da ya gabata Sudan ta nuna shirin amincewa da girke dakarun amma ba´a tantance kasar da zata jagoranci rundunar ba.