Sudan ta amince da girke dakarun AU da na MDD a Darfur | Labarai | DW | 12.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta amince da girke dakarun AU da na MDD a Darfur

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon yayi maraba da amincewar da Sudan ta yi na girke rundunar hadin guiwa ta kungiyar tarayyar Afirka da MDD a lardin Darfur. Mista Ban Ki Moon ya kuma jaddada bukatar da ke akwai ta tsagaita wuta nan take a yankin da yaki ya daidaita. Ban ya ce dole ne kuma shirin warware rikicin yankin na Darfur ya biyo bayan tsagaita wutar. Wata sanarwar hadin guiwa da suka bayar yau talata a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha kungiyar AU da MDD sun ce gwamnati a birnin Khartoum ta amince da shirin girke dakarun hadin guiwa bayan an yi mata bayani dalla-dalla daga kungiyoyin guda biyu. Kawo yanzu sojoji dubu 7 da kungiyar AU ta girke a Darfur sun kasa magance ayyukan assha da kisan gilla da ake yi a wannan lardi dake yammacin kasar Sudan. A bara gwamnatin Sudan ta amince da kara yawan sojojin amma daga baya sai ta bijire.