Sudan ta amince da aika dakaru zuwa Darfur | Labarai | DW | 13.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta amince da aika dakaru zuwa Darfur

Kasar Sudan ta amince a aike da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da AU zuwa yankin Darfur sai dai kuma kasar Amurka ta baiyana shakkunta game da ko gwamnatin Sudan din zata bi kaidojin wannan yarjejeniya.

Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen Amurka Sean McCormack yace shugaban kasar Sudan Umar al-Bashir ya gagara cika alkawura daya dauka a baya.

Rundunar ta MDD da AU zata kunshi sojoji da yan sanda fiye da 20,000 yawancinsu daga kasashen Afrika.

Rikicin na Darfur ya halaka akalla mutane 200,000 wasu kuma miliyan 2.5 suka tagaiyara.