Steinmeir a Afghanistan
May 22, 2007A ƙalla sojojin gwamnati 4 da yan taliban 10, su ka rasa rayuka a cikin hare-hare daban-daban, da su ka wakana a gabas da kudancin ƙasar Afghanistan.
A cikin wanan yanayi ne, ministan harkokin wajen ƙasar Jamus, Frank Walte Steinmeir, ya kai ziyara ƙasar, domin ƙara ƙarfin gwiwa ga sojojin Jamus.
Idan dai ba amanta ba 3 daga wanansojoji su ka rasa rayuka sannan wasu ƙarin 4, su ka ji raunuka, a cikin harin da wani ɗan ƙunar bakin wake, ya abkawa masu, a birnin Kunduz.
Nan gaba a yau, Steinmeir zai gana da shugaban Afghanistan Hamid Karzai, domin tantanawa, a game da halin da ake ciki a wannan ƙasa, da ke fama da tashe-tashen hankulla, tun korar yan taliban daga mulki, a shekara ta 2003.
Baki ɗaya, ƙasar Jamus, na da sojoji dubu 3, a arewancin ƙasar Afghanistan, kuma harin baya-bayan nan da a ka kai masu, shine mafi muni, tun zuwan su ƙasar a shekara ta 2003.