Steinmeier zai kai ziyara a birnin Beirut. | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Steinmeier zai kai ziyara a birnin Beirut.

Ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, zai tashi yau zuwa Lebanon, tare da wasu jami’an tsaron iyaka da na kwastam na nan Jamus, waɗanda za su taimaka wajen inganta matakan tsaro a filin jirgin saman birnin Beirut. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a wata ziyarar da ya kai a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya, Steinmeier, ya ce Jamus za ta ba da gudummowar jami’ai guda 10, don su taimaka wajen gudanad da binciken fasinjoji da kaya a filin jirgin saman Beirut ɗin. Burin yin hakan dai shi ne rage kasadar yin fasa ƙwaurin makamai zuwa ga ƙungiyar Hizbullahi.

Har ila yau dai babu tabbas kan lokacin da majalisar ministocin gwamnatin Angela Merkel, za ta yi taron yanke shawara kan tura jiragen ruwan yaƙin Jamus zuwa Lebanon ɗin.