1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier ya bukaci Turkiyya ta yi adalci

November 4, 2016

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nuna rashin jin dadi kan dirar mikiyar da Turkiyya ta yi wa jam'iyyar adawa ta HDP tare da kame wasu 'ya'yanta a majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/2SAky
Frank-Walter Steinmeier in Luxemburg
Hoto: DW/B. Riegert

Gwamnatin Jamus ta bukaci Turkiyya ta yi adalci ga mutanen da ta kama 'yan jam'iyyar Kurdawa ta HDP. 'Yan sanda sun kai samame gida-gida tare da kame wasu shugabannin jam'iyyar HDP, wadda ita ce jam'iyya ta biyu mafi girma a majalisar dokokin kasar.Tun da farko an kama 'yan majalisar dokokin jam'yyar su tara a ranar Juma'ar nan bayan da suka ki bada bahasi kan zargin wata farfaganda da ta danganci ta'addanci. Ita ma kungiyar tarayyar Turai ta baiyana matukar damuwa da tsare shugabannin adawa da gwamnatin Turkiyyar ta yi. A cikin wata sanarwa babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turan Federica Mogherini ta soki lamirin cire rigar kariya ga 'yan majalisar dokokin wanda ya bai wa gwamnati damar tsare 'yan majalisar na bangaren adawa.