Steinmeier ya buƙaci cigaba da matakan diplomasiya | Labarai | DW | 06.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Steinmeier ya buƙaci cigaba da matakan diplomasiya

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier yace baá sami wani cigaba ba a ganawar sa da babban mashawarcin Iran Ali Larijani a birnin Berlin da nufin kawo ƙarshen kiki-kaka da ake yi kan shirin Iran na makamashin Nukiliya. Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar Steinmeier, yace akwai buƙatar cigaba da matakai na diplomasiya domin jawo raáyin Iran ta dakatar da bunƙasa sinadarin Uranium. Kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ya yi kurarin sanyawa Iran ƙarin tsauraran takunkumi idan ta ƙi bin umarnin da aka yi mata. Ƙasashe da dama na yammacin turai na fargabar cewa Iran na mallakar makamai ne na ƙare dangi. Ita kuwa Tehran ta dage cewa shirin na nukiliya na lumana ne.