Steinmeier da Fischer sun ce ba su da masaniya game da zargin sace wani Bajamushe ba | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Steinmeier da Fischer sun ce ba su da masaniya game da zargin sace wani Bajamushe ba

Ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier da magabacinsa Joschka Fischer sun musanta cewa suna da wata masaniya game da garkuwar da hukumar leken asirin Amirka CIA ta yiwa wani haifaffen Jamus. Dukkan mutanen biyu sun fadawa wani kwamitin bincike na majalisar dokoki cewa zargin da ak yi musu bai da tushe bare makama. A karshen shekara ta 2003 aka kame Khalid el-Masri Bajamushe dan asalin Libanon a Macedoniya sannan daga bisani aka tura shi wani sansanin hukjmar CIA dake Afghanistan kafin a sake shi a shekara ta 2004. A wancan lokaci Fischer ne ministan harkokin wajen Jamus yayin Steinmeier ke jagorantar wani ofis a fadar tsohon shugaban gwamnati Gerhard Schröder.