1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier a Jakakarta,Indonesiya

Zainab MohammedFebruary 27, 2008

Ziyarar ministan harkokin wajen Jamus a ƙasar Indonesiya

https://p.dw.com/p/DEYD
Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier,da takawansa na Indonesiya Hassan Wirajuda.Hoto: AP
Ministan harkokin wajen jamus Fran-kwalter Steinmeier yana ƙasar Indonesia, wadda ke zama kafar sa ta farko a rangadin aikin kwanaki biyar ,daya keyi a yankin Asia,ziyarar da keda nufin bunkasa dangantakar siyasa da tattalin arzikin ɓangarorin biyu. A birnin Jakarta dake zama fadar gwamnatin Indonesia,Frank-Walter Steinmeier yayi kiura na musamman ga gwamnatin ƙsar data cigaba da taka rawa dangane da kokarin da akeyi na shawo kan Iran,yin watsi da shirin Nukiliyan ta. ƙasashe biyar dake da zaunanniyar kujera a komitin sulhu na Majalisar Ɗunkin Duniya tare da Jamus,a 'yan makonni da suka gabata sun gudanar da tattaunawa a birnin Berlin dangane da yiwuwar kakabawa Tehran sabbin takunkumi domin labatar da ita. A tattaunawar sa'a ɗaya tsakanin ministan harkokin wajen na Jamus da takwaran sa na Indonesia Hassan Wirajuda,ɓangarorin biyu sun taɓo batutuwa da dama musamman waɗanda suka shafi dangantakarsu,da kuma yiwuwar inganta ta. Steinmeier yayabawa kokarin Indonesi bisa ga tabbatar da Demokraɗiyya a wannan kasa ta musulmi. "Yace muna darajawa namijin kokarin wannan kasa,domin komawa tafarkin demokraɗiyya da komawa gudanarwa da mulki bisa kundun tsarin mulki ,ba abubuwa ne masu sauki ba,da ta fara tun a shekaru 10 da suka gaba,don haka muna jinjina mata" Shi kuwa minisatn harkokin wajen Indonesia Hassan Wirajuda,yabawa dangantakar ƙashen biyu yayi,sai dai acewar sa Indonesia na bukatar karin tallafin Jamus ta fannin inganta Democraɗiyya da harkokin kasuwanci.Ya kumayi amfani da wannan dama wajen kira ga jamus data cigaba da gudanar da harkokin kasuwanci da Indonesia,kasancewar Steinmeier yana wannan rangadi ne da tawagar wasu yan kasuwan jamus.... "Minista Hasan yace,Ina ganin tunda Indonesia tana samun cigaba a ɓangarori daban-daban,bawai a harkokin Demokraɗiyya kawai ba,amma harda ɓangaren tattali,kasancewar tattalin arzikimmu na cigaba da samun bunkasa ,nayi imanin cewar hakan zai kara mana daman cuɗanya da abokammu na tarayyar Jamus,domin samun karuwar dangantaka ta fannin tattali" Adangane da halin da ake ciki a kasar Myanmar kuwa ,ministan harkokin wajen na Indonesia Wirajuda yace suna kokarin ganin cewar gwamnatin sojin kasar ta cikanta alkawura data ɗauka na girka mulkin Demokraɗiyya... "Yankin Asia baki ɗaya,ko kuma Indonesia suyi ciɗayya da Myanmar domin tabbatar dacewar,matakin datake shirin ɗauka yanzu na shiya sabon kundun tsarin mulki ,kana daga baya ta gudanar da zaɓe,zai kasance batutuwa ne da aka gudanar bisa ga karɓuwa a idanun ƙasashen duniya." Akan rikicin Nukiliyan ƙasar Iran ,wadda ayanzu ƙasashen turai ke kokarin zartar da kudurin kara ɗaukar matakan ladabtar da ita daura da komitin sulhu na Majalisar Ɗunkin Duniya,ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier ya nemi goyon Indonesia wajen shawo kan Tehran... "Muna kira ga Indonesia,saboda tasirin da take dashi tsakanin duniyar musulmi ,data tabbatar da haɗin kai a tsakanin ƙasashen,domin hakan ne zai samarda tsaro na kasa da kasa.Muna neman goyon bayan ta adangane da kokarain da ake cigaba game da Iran,domin ganin cewar ta dakatar da shirin Nukiliyan ta,wanda hakan ne zai maido da ita tsakanin ƙasashen duniya" Adangane da matsalolin ɗumamayr yanayi da hanyoyin kalubalantar sa,ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier yayi kira ga Indonesia data daɗa matsa kaimi wajen ɗaukar matakai na kare alummarta.Jamus dai ta bawa Indonesiyan tallafin Euro Million 24. Daga Indonesiyan dai Steinmeier zai shige Singapore kana Vietnam kafin ya komo tarayyar jamus.