Steinmeier a Gabas Ta Tsakiya | Siyasa | DW | 01.06.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Steinmeier a Gabas Ta Tsakiya

Bundesaußenminister Steinmeier bricht am Samstagabend zu einer dreitägigen Reise in den Nahen Osten auf. Erste Station ist Libanon. Anschließend reist Steinmeier nach Israel und in die Palästinenser-Gebiete weiter.

default

Steinmeier da shugaban Lebanon Michel Suleiman

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinemeier ya ce ya ga kyawawan alamu masu ƙarfafa guiwa a Lebanon. Ministan ya bayyana haka bayan ganawarsa da sabon zaɓaɓɓen shugaban Lebanon Michel Suleiman a birnin Beirut, zangon farko a rangadin kwanaki uku da Steinmeier ɗin ke yi a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Wannan ziyarar dai ta ministan harkokin wajen na Jamus Frank Walter Steinmeier ta zo ne a daidai lokacin da ake ci-gaba da zaman ɗar-ɗar a birnin Beirut, inda sojoji suka kafa sansanoni a muhimman wurare a babban birnin na Lebanon sannan motoci masu sulke ke yi ta sintiri. Sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Doha a ranar 21 ga watan Mayu yanzu ƙasar ta samu majalisar dokoki dake aiki wadda ta zaɓi shugaban ƙasa wato Janar Michel Suleiman.


A matsayin wani babban jami´in farko na wata gwamnatin ƙasar yamma da ya kai ziyara Lebanon tun bayan zaɓen Michel Suleiman a matsayin sabon shugaban ƙasar, Steinmeier ya yaba da aniyar sabon shugaban ta nuna goya baya ga kotun ƙasa da ƙasa da zata yi shari´ar mutane da ake zargi da hannu a kisan gillan da aka yiwa tsohon firaminsitan Lebanon Rafik Hariri da kuma wasu ´yan siyasar ƙasar dake adawa da Syria. Ya tabbatarwa shugaban taimako na sake gina hukumomin gwamnatin Lebanon.


Steinmeier ya ce "Za mu yi iya ƙoƙarinmu daga Turai da kuma Jamus domin mu tallafawa wannan shiri na gwamnati. Janye wuraren da aka toshe hanyoyi a Beirut da zaɓen sabon shugaban ƙasa da kuma shirin kafa sabuwar gwamnati cikin kwanaki ko makonni dake tafe abubuwa ne masu ƙarfafa guiwar al´ummar Lebanon."


Kafin ya bar Lebanon Steinmeier ya kai ziyara a sansanin da aka girke sojojin Jamus a gaɓar tekun ƙasar don hana masu sumogar makamai cikin Lebanon.


Zango na gaba a wannan rangadi shi ne Isra´ila inda duk wani fata na farfaɗo da shirin wanzar da zama lafiya ke ƙara dushewa. Ziyarar ta sa a Isra´ila ta zo ne a cikin wani hali na rashin sanin tabbas dangane da rikicin siyasa na cikin gida a Isra´ila inda firaminista Ehud Olmert ke fsukantar kiraye kiraye da yayi murabus sakamakon zargin cin hanci da rashawa. Tattaunawar da Steinmeier zai yi da shugabannin Falasɗinawa kuwa ita ce ta 11 amma ba ya jin zata haifa da wani kyakkyawan sakamako.


"Har yanzu dai babu alamun cimma wata yarjejeniya kafin ƙarshen wannan shekara. Babu dai wata alama dangane da haka."


A kan hanyarsa ta komawa Berlin Steinmeierzai yada zango a birnin Riga na ƙasar Letvia inda zai halarci taron ƙolin ƙasashen yankin gabashin gaɓar Tekun Arian don tattauna batu n shimfiɗa bututun mai zuwa Jamus.