Steinmeier a Alkahira | Siyasa | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Steinmeier a Alkahira

Ala tilas ministan harkokin wajen Jamus ya katse ziyararsa ga Yankin Gabas ta Tsakiya

Steinmeier

Steinmeier

Matsaloli masu tarin yawa suka dabaibaye yanayin ziyarar ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier a kasar Masar. A daura da ganawarsa da takwaransa ministan harkokin wajen kasar Masar Ahmed Abul Gheit an sha fama da tababa a game da yadda ministan harkokin wajen na Jamus zai fuskanci soke-soken da za a yi masa a majalisar dokoki ta Bundestag a gobe juma’a dangane da hannu dumu-dumu da yake da shi a tabargazar nan da ta shafi rawar da hukumar leken asiri ta BND ta taka a yakin Iraki. Duk da gajiyar dake tattare da shi, amma ministan harkoki wajen Frank-Walter Steinmeier a cikin gadin gaba ya rika amsa tambayoyin da manema labarai suka rika fuskantarsa da shi sannan ya ce zai shiga zauren mahawarar majalisar dokokin ta Bundestag ne tattare da kwarin guiwa. Steinmeier ya kara da bayani yana mai cewar:

„Shawarar da gwamnati ta tsayar ta hada ne da sharadin cewar Jamus ba zata tsinke kawancenta da Amurka ba, abin da ya hada da ba wa Amurkan cikakkiyar dama ta ci gaba da tsugunar da sojojinta a sansanoninta dake harabar Jamus kazalika da ci gaba da hadin kai tsakanin hukumomin leken asirin kasashen biyu. Babu wani abin da zai shafi wannan batu. Kuma a saboda haka a gani na babu wani dalili a game da zargin da wasu wakilan majalisar dokokin ke yi mana.“

Hukumar leken asirin Jamus ta BND ta tsugunar da wasu jami’ant guda biyu a birnin Bagadaza a lokacin yakin Iraki, kuma tsofuwar gwamnatin kasar ta Jamus tana da cikakkiyar masaniya game da haka. Sabanin da ake yi a yanzun shi ne, ko Ya-Allah hukumar leken asirin ta Jamus ta mika wasu bayanai domin taimaka wa sojan Amurka wajen kai hare-hare a wasu zababbun wurare a Irakin. A wancan lokaci dai Steinmeier ne shugan ofishin shugaban gwamnati kuma mai kula da al’amuran leken asirin kasa, amma a yanzun a ganinsa ‚yan hamayya na nema da su kalubalance shi ne ba akan gaskiya ba. Steinmeier zai shiga wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi idan har majalisar dokoki ta Bundestag ta tsayar da shawarar kafa wani kwamitin bincike da zai bi bahasin wannan tabargaza. A ziyarar tasa ga kasar Masar, a yau alhamis ministan harkokin wajen na Jamus zai gana da shugaba Husni Mubarak inda zasu tabo matsayin KTT dangane da shirin makamashin nukiliya na kasar Iran da sauran matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa a Yankin Gabas ta Tsakiya.