1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soyinka zai ɓullo da sabuwar jam'iyya

July 20, 2010

Wole Soyinka ya ce zai samar da jam'iyyar siyasar da za ta kawo ƙarshen cin hanci a Nijeriya

https://p.dw.com/p/OQLh
Hoto: AP

Sanannen marubucin adabinnan a Nijeriya, wanda ya taɓa karɓar lambar yabo ta NOBEL Wole Soyinka, ya bayyana cewar yana shirin ɓullo da jam'iyyar siyasa, bayan shekarun daya kwashe yana yin suka ga matsalar cin hanci da rashawa da kuma yadda ake gudanar da harkokin gwamnati a ƙasar sa ta haihuwa, wadda ke da ɗimbin albarkatun man fetur.

A cikin wani taƙaitaccen jawabin da yayi wajen bukin cikar sa shekaru 76 da haihuwa Soyinka ya ce yana da muradin ƙafa jam'iyyar masu ra'ayin ci gaba, wadda kuma za ta yi takara a zaɓukan ƙasar da ake sa ran zai gudana a farko - farkon shekara mai kamawa idan Allah ya kaimu. Soyinka ya ƙara da cewar a watan Satumba ne zai ƙaddamar da sabuwar jam'iyyar tasa, tunda a cewar sa masu mulki a yanzu sun gaza biyan bukatun jama'a.

Shi kuwa Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin Nijeriya ta'anniti ta EFCC wanda ya gabatar da jawabi a wajen bukin zagayowar ranar haihuwar Soyinka cewa ya yi cin hanci ne ya hana Nijeriya cin gajiyar ɗimbin arziƙin man fetur ɗin da Allah ya hore mata, kasancewar wasu shugabanni na karkata akalar kuɗin da ƙasar ke samu daga man fetur.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal