1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somi-somin juyin-juya hali a Zimbabuwe

Yusuf BalaAugust 28, 2016

Shugaba Robert Muhgabe ya yi gargadin kada masu bore a kasarsa su kuskura su kwatanta abin da ya faru a kasashen Larabawa wato a lokacin juyin juya hali.

https://p.dw.com/p/1JrEm
Simbabwe Harare Proteste gegen Präsident Mugabe
Dubban al'umma ne a kasar ta Zimbabuwe ke fitowa dan nuna adawa da salon mulkin MugabeHoto: picture-alliance/AA

A kasar ta Zimbabuwe 'yan sanda ne ke ci gaba da kame-kame na masu zannga-zanga a birnin Harare da kawowa yanzu an cafke mutane 67.

Shugaba Mugabe a cewar gidan jaridar Herald su mutane ne masu son zaman lafiya kada wani ya takalo su su fusata a kan al'umma.

Shugaban ya bayyana haka a lokacin da yake sallamar wasu dalibai na kasar da za su tafi kasar China dan karatu. Har zuwa Asabar an ci gaba da samun masu zanga-zangar a titunan kasar inda su kuma a nasu bangaren jami'an tsaro ke baza masu zanga-zangar adawa da mulkin na Mugabe ta hanyar baza su da kulake da hayaki mai sa hawaye banda wadanda aka garkame a hannun jami'an tsaro.