Somaliya shekara daya bayan tsunami | Siyasa | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Somaliya shekara daya bayan tsunami

Kasar Somaliya na daga cikin kasashen da bala'in tsunami ya rutsa dasu

Somaliya bayan tsunami

Somaliya bayan tsunami

Kasar Somaliya mai fama da yamutsin siyasa da ta’asar ‚yan ta-kife ba zata samu wani kyakkyawan matsayi a kundin tarihin kasashen da bala’in tsunamin yayi kaca-kaca da su ba, duk da asarar rayuka da kadarori da tayi da kuma mawuyacin halin da mazauna yankunan gabar tekun kasar suka samu kansu a ciki. Kungiyoyin agaji sun kiyasce yawan mutanen da suka yi asarar rayukansu sakamakon bala’in na tsunami a Somaliya zai kai mutum 300 sai kuma wasu dubu 33 da suka tagayyara a gabar tekun kasar mai tsawon kilomita 650. Amma fa wannan bala’in ya kara tsaurara mawuyacin hali ne da al’umar Somaliya ke ciki. Kasar ta fuskanci matsaloli na ambaliya sakamakon ruwan sama da aka rika yi kamar da bakin kwarya, bayan bala’in farin da ya rutsa da ita. Kuma tun mutane ba su sarara daga wannan matsala ba bala’in tsunami ya ratsa kasar ta Somaliya a daidai ranar 26 ga watan desamban bara. Kungiyar taimakon abinci ta MDD ita ce ta farko da ta kai agaji ga mutanen da bala’in ya rutsa da su. A lokacin da yake bayani game da halin da jama’a suka kasance a lardin Putland mai ikon cin gashin kansa a arewa-maso-gabacin Somaliya, Leo van der Velden, mataimakin shugaban kungiyar taimakon abinci ta MDD a wannan yanki, cewa yayi:

„Bala’in ya fi tsanani a tsuburin Harfun, wanda gaba daya ruwa ya mamaye shi. Ambaliyar tayi kaca-kaca da gidajen mutane ta kuma bannatar da kwale-kwalensu da sauran kayayyakinsu na kamun kifi, wanda suka dogara akansa a rayuwarsu ta yau da kullum.“

Dangane da masu kamun kifin da bala’in tsunamin ya cimmusu a bakin aikinsu kuwa kaddara ta rutsa dasu, babu daya daga cikinsu da ya dawo gida. Ambaliyar, kazalika ta bannatar da dukkan hanyoyin sadarwa a wannan yanki, lamarin da ya sanya aka fama da wahala wajen kai taimako ga mutanen da lamarin ya shafesu. Kungiyoyin agaji sun shiga amfani da jiragen ruwa domin kai taimakon abinci da magunguna da barguna ga jama’a. A baya ga kungiyar taimakon abinci ta MDD shi ma asusun taimakon yara na majalisar UNICEF a takaice har yau yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na taimako kafada-da-kafada tare da sauran kungiyoyin taimako masu zaman kansu kamar kungiyar Muslim Aid domin gina gidaje da makarantu da kuma sake farfado da hanyoyin sadarwa a yankunan kasar Somaliya da bala’in na tsunami ya rutsa da su a wajejen karshen shekarar da ta wuce.