Somalia | Labarai | DW | 08.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somalia

‚Yan majalisar dokokin kasar Somalia sun zartar da dokar dake bawa wadanda ba ‚yan majalisa ba damar samun mukamai na ministoci.Amincewa da wannan doka zata bawa shugaban kasar damar nadin wanda zai maye gurbin premiern Ali Mohammed Gedi.Kakakin Majalisar Sheikh Adan Madobe ya fadawa ‚yan majalisa sama da 200 cewar,dukkanin su sun amince da wannan doka bayan yini uku na mahawara.’Yan majalisar Somalian dai sun jaddada bukatar gaggauta amfani da wannan doka wajen nadin sabon prime minista,dazai maye gurbin Gedi.A kwanaki 10 da suka gabata nedai Premier Ali Mohammed Gedi yayi murabus daga mukaminsa,bayan sabanin daya wakana tsakaninsa da shugaba Abdullahi Yusuf,wanda ya kawo tsaiko a harkokin gwamnatin wannan kasa ta Kahon Afrika,dake fama da tashin hankalin yan adawa a birnin Mogadishu.