Somalia ta zargi abokan gaba da kokarin ta da zaune tsaye a cikin kasar | Labarai | DW | 24.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somalia ta zargi abokan gaba da kokarin ta da zaune tsaye a cikin kasar

Sojojin sa kai na Islama da suka kwace iko a babban birnin Somalia sun ce wata abokiyar gaba ta ketare wadda ke son ganin kasar ta sake tsunduma cikin hargitsi bayan an shafe ´yan makwanni kalilan ana zaman lafiya, ta shirya kisan da aka yiwa wani dan jaridar Sweden. A gun wani taron gangami da aka yi jiya a birnin Mogadishu aka harbe Martin Adler mai shekaru 47 har lahira. A yau asabar wani jirgin saman kungiyar ba da agaji ta Red Cross ya yi jigilar gawarsa zuwa Nairobi babban birnin kasar Kenya kafin a karasa da ita zuwa Sweden. Shugaban kungiyar kotunan Islama, Sheikh Sharif Sheikh ya ce an shirya kisan ne daga wajen kasar da nufin ta da zaune tsaye a Somalia. To sai dai bai yi karin bayani ba.