Somalia ta yi tayin yiwa mayakan Islama afuwa | Labarai | DW | 19.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somalia ta yi tayin yiwa mayakan Islama afuwa

Gwamnatin Somalia ta yi tayin yin afuwa ga ´ya´yan kungiyar Islama wadanda suka mulki yankin kudancin kasar na tsawon watanni 6 a bara. Wata sanarwa da gwamnati a birnin Mogadishu ta bayar ta ce hakan wata alama ce ta fatan alheri gabanin taron samar da zaman lafiya da za´a yi cikin wata mai zuwa. Sanarwawar ta zo ne sa´o´i kalilan bayan an bindige kakakin shugaban kasa a wuya a lokacin da yake cikin wani cunkoson motoci a wannan kasa mai fama da rikice rikice. Lokacin da yake karantar sanarwar wadda shugaba Abdullahi Yusuf ya rattabawa hannu, ministan shariá Hasan Dhimbil Farah ya ce shugaban ya amince ya yiwa sojojin sa kai wadanda ke yakar dakarun gwamnati afuwa kuma gwamnati zata saki tsoffin ´yan tawaye daga gidajen kurkuku.