Somalia ta nemi Ethiopia ta ƙara mata taimakon soji | Labarai | DW | 07.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somalia ta nemi Ethiopia ta ƙara mata taimakon soji

Bayan tashe tashe hankulan da aka fuskanta jiya a Mogadishu babban birnin Somalia, kafofin yada labaru sun rawaito gwamnatin wucin gadi na rokon Ethiopia da ta kara ba ta taimakon soji. Gidan telebijin Ethiopia ya labarto cewa FM Ethiopia Meles Zenawi yayiwa shugaban Somalia Abdullahi Yusuf alkawarin ba shi taimakon horas da sojojin Somalia. Dukkan shugabannin biyu sun yi kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta gaggauta ba da taimakon sake gina Somalia. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce akalla mutane 3 sun rigamu gidan gaskiya a wani hargitsi da aka yi jiya yayin wata zanga zangar nuna adawa da Ethiopia a birnin Mogadishu. ´Yan sanda sun ce mutum daya ya rasa ransa.