1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Solana da Larijani sun gana a birnin Vienna.

September 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buk3

Babban jami’in kula da harkokin ƙetare na Ƙungiyar Haɗin Kan Turai Javier Solana, ya gana da jagoran tawagar Iran a kan batutuwan makamashin nukiliya Ali Larijani a birnin Vienna na ƙasar Austriya. Wata kakakin ƙungiyar EU ta ce an sani kyakyawan sakkamamko a shawarwarin. A yau ne dai jami’an biyu za su ci gaba da tattaunawarsu. Za su mai da hanakalinsu ne kan farfaɗo da shawarwari kan tayin da ƙasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Jamus suka yi wa Iran ɗin. Iran dai ta yi watsi da wa’adin da kwamitin sulhu na majalisar ya ba ta na ta dakatad da duk ayyukan sarrafa sinadarin Yureniyum kafin ran 31 ga watan Agustan da ya gabata, in ko ba haka ba, a sanya mata takunkumi.

Amirka kuma, na neman a zartad da sabon ƙuduri a mako mai zuwa, na sanya wa Iran ɗin takunkumi.