1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke tashin jiragen sama a Turai ya shafi Afirka

April 23, 2010

Soke tashin jiragen sama a Turai ya shafi tattali arzikin ƙasashen Afirka

https://p.dw.com/p/N55q
Hoto: AP

A wannan makon dai batun hanin sauka da tashin jiragen sama da aka fuskanta a ɗaukacin ƙasashen Turai sakamakon aman wuta da wani dutse a ƙasar Iceland yayi ya fi ɗaukar hankalin jaridun, inda wasu suka nuna illar da hakan yayiwa tattalin arzikin wasu ƙasashen Afirka. A rahotonta mai taken An samu tsaiko a harkar cinikiya tsakanin ƙasa da ƙasa, jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa rufe sararin samaniyar nahiyar Turai ga zirga-zirgar jiragen sama ya gurgunta hada-hadar cinikaiyar duniya kana kuma ya haddasa asarar dubbannen miliyoyin daloli ga Asiya da Afirka. Ta ba da misali da mummunan koma-bayan kuɗaɗen shiga a wasu ƙasashen Afirka kamar Kenya da ke samarwa kasuwannin Turai da furanni da 'ya'yan itace da a bara ya samarwa ƙasar dake gabacin Afirka dala miliyan 700. To amma saboda matsalar rashin zirga-zirgar jiragen sama, a dole ƙasar ta zubar da aƙalla tan 1000 na wannan hajjar a kowace rana yayin da ma'aikata kuma suka shiga zaman kashe wando. Su ma ƙasashen Ehiopiya da Zambiya dake samar da furanni ga ƙasashen Turai sun fuskanci wannan koma-baya yayin da Senegal dake aikewa da ɗanyen kifi zuwa nahiyar Turai ita ma ta yi asara musamman saboda rashin manyan injunan adana kifin.

Fußball WM Südafrika 2010 Pretoria Werbung
Hoto: DW

'Yan wariyar launin fata na son yiwa gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya zagon ƙasa, taken rahoton da jaridar Frankfurter Rundschau ta rubuta kenan tana mai nuni da farar fatar Afirka Ta Kudu masu matsanancin ra'ayi dake shirin kai hare hare a lokacin wasan cin kofin ƙwallon ƙafa. Jaridar ta rawaito 'yan sandan Afirka ta Kudu na cewa sun bankaɗo wata maƙarƙashiya da ƙungiyar kishin farar fata Suidlanders ke yi na janyo ruɗami a lokacin gasar. Yanzu haka dai 'yan sandan sun ce sun ƙwace tarin makamai daga ƙungiyar. A shafinta na yanar gizo ƙungiyar ta Suidlanders tana kira da a ƙauracewa gasar da za a fara cikin watan Yuni. Ƙungiyar ta ce tura ta kai bango game da irin wulaƙanci da fararen fatu ke fuskanta yanzu a Afirka Ta Kudu ke yiwa 'ya'yanta.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci ne game da garkuwar da wasu 'yan bindigar yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a Najeriya ta yiwa wasu Jamusawa biyu. Ta ce bisa dukkan alamu dai faɗan 'yan tawayen ne ya rutsa da Jamusawa. Ta ce a kowace shekara ana garkuwa da baƙi ko masu hannu da shuni a yankin na Niger Delta, inda ake ba da kuɗin fansa kafin a sake su ba tare da an yi musu ko ƙwarzami a jiki ba.

Somalia Mogadischu Islamisten Flüchtlinge
Hoto: AP

Babu ɓangaren dake ba da kariya a yaƙin da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Somaliya, inji jaridar Die Tageszeitung, inda ta ƙara da cewa Somaliya ce ƙasa ɗaya a duniya inda wani rukuni na 'yan ƙasar suka tashi ba tare da wata tsayayyar hukuma ba. Ta ce shekaru 19 kenan babu gwamnatin tsakiya a ƙasar, inda yanzu 'yan tawaye da sojojin gwamnatin riƙon ƙwarya ke fafatawa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi