1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojojin Iraki na samun nasara a Mosul

October 20, 2016

Sojojin gwamnati da ke samun goyon bayan dakarun kundunbala na Kurdawa na ci gaba da dannawa izuwa karshen tungar mayakan IS, da ke birnin Mosul inda tuni suke samun nasaran kwace wasu yankuna.

https://p.dw.com/p/2RV2g
Irak Konflikte
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye

Mayakan kundumbala da ke fafatawa da mayakan IS a birnin Mosul, sun bayyana samun nasarar karbe iko da garin Bartalla da ke gabashin kasar. Sama da shekaru biyu kenan dai kawo yanzu wannan karamin gari da mafi yawan ci mazauna yankin kiristoci ke karkashin ikon mayakan na IS. Wani kwamandan dakarun kwancen ya bayyana yadda sojojin ke samun galaba a kan mayakan na IS a birnin na Mosul dake zama birni na biyu mafi girma a Irakin da ya shiga hannun mayakan sama da shekaru biyu.

A yanzu dai dakarun na Iraki na ci gaba da wallafa hotunan bidiyo da ke nuna yadda suke samun galaba na kwace iko da wasu kauyuka daga yankin kudu da gabashin kasar. Andai yi kiyasin akall fararen hula sama da 5,500 ne tsamin wuta a birnin na Mosul ya tilastawa ficewa daga matsugunansu cikin kwananki uku da dakarun hadin guiwa suka kaddamar da yakin kwace birnin.