1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Yemen sun fatattaki 'yan Al-Qaida

A kokarin da suke na kakkabe 'yan ta'addan Al-Qaida da suka mamaye wasu yankunan kasar, jami'an tsaron kasar Yemen na ci gaba da samun nasara kan mayakan.

Sojoji da 'yan sanda na kasar Yemen sun kori mayakan kungiyar Al-Qaida da ga birnin Houta da ke a matsayin babban birnin jihar Lahj a Kudancin kasar a wannan Jumma'a a cewar wata majiya ta jami'an tsaro.

Dakarun dai sun tashi ne daga birnin Aden zuwa Houta da ke a nisan km 30, inda suka kwaci wasu gine-gine na gwamnati tare da korar mayakan na kungiyar Al-Qaida da suka yi kaka-gida a wannan birni, kuma an samu kama wasu mayakan na 49 a cewar majiyar.

Kafin dai wannan mataki, sai da jiragen yaki na kasashen kawance da Saudiyya ke yi wa jagoranci suka shafe kwanaki biyu suna luguden wuta kan mayakan.