Sojojin Ukraine sun halaka a fada da ′yan tawaye | Labarai | DW | 17.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Ukraine sun halaka a fada da 'yan tawaye

An dai bada rahotannin cewa an ji fada ya yi tsamari a kusa da garin Avdiivka daga Arewaci da Marinka daga Yammaci na birnin Donetsk da 'yan awaren ke da karfi a cikinsa.

Sojojin Ukraine uku sun halaka yayin da goma suka samu raunika bayan wani fada tsakaninsu da 'yan tawaye da ke samun goyon bayan kasar Rasha kamar yadda jami'an sojan kasar suka bayyana a ranar Juma'an nan.

An dai bada rahotannin cewa an ji fada ya yi tsamari a kusa da garin Avdiivka daga Arewaci da Marinka daga Yammaci na birnin Donetsk da 'yan awaren ke da karfi a cikinsa.

Gwamman mutane ne dai suka halaka a makonnin baya-bayan nan, bayan da fada ya yi kamari tsakanin bangarorin da ba a ga maciji tsakanin juna, abin da ke zuwa a daidai lokacin da kasar ta Ukraine ta karbi jagoranci na karba-karba na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar hadin kai da tsaro a tsakanin kasashen na Turai (OSCE) da ke sanya idanu kan rikicin Gabashin na Ukraine ta bayyana cewa fadan ya yi kamari a farkon wannan wata sai dai ya sake lafawa kamar yadda aka saba gani a yankin.

A ranar Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen Ukraine da Rasha da Jamus da Faransa za su gana a wani bangare na taron tsaro na kasa da kasa da akla fara a birnin Munich na nan Jamus.