1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Tchad sun shiga farautar yan tawaye

Bayan saban yunƙurin juyin mulkin da yan tawaye, su ka buƙaci shirya wa shugaba Idriss Deby na Tchadi,a makon da ya gabata, a ranar jiya sojoji masu biyyaya ga gwammnati, sun fara farautar yan tawayen da ke gabancin wannan ƙasa.

Kommamadan dakarun sojojin ƙasar, ya bayyana cewa, a ranar yau talata, sun samu nasara fattatakar ɗaya daga sassanin yan tawaye, da ke tsaunukan Hadjer Marfain, inda kuma, su ka girka rundunar soja, domin maido doka da oda a yankin.

Shugaban ƙasa Idiss Deby, da kansa a matsayin sa na massani a kan al ´ammuran yaƙi, ke jagorantar hare haren, da sojojin gwamnati, ke kaiwa yan tawaye.

A baya bayan nan, shugaban ƙasar Tchadin na tare da ƙarancin kwanciyar hankali, dalili da murabus ɗin, da sojojin ke ci gaba da yayi, domin sadewa da yan tawaye, da su ka sha alƙawarin kiffar da shugaba Idriss Deby, da ya ɗare karagar mulki, tun shekaru 16 da su ka wuce.