Sojojin Syriya na samun galaba a Aleppo | Labarai | DW | 28.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Syriya na samun galaba a Aleppo

Dakarun gwamnatin Syriya tare da hadin gwiwar sojojin kawance da ke fafatawa a gabashin birnin Aleppo sun bayyana kwace manyan yankuna masu muhimmaci da ke hannun 'yan tawayen kasar.

Wata kafar yada labarun kasar Syriya ta ruwaito cewa gundumar Sakhour na cikin yankuna 10 tare da manyan gine gine 3,000 da a yanzu ke karkashin ikon dakarun gwamnatin Bashar al-Assad. Wata sanarwa da ma'akatar tsaron kasar Rasha ta fitar na cewa daruruwan 'yan tawaye na yada makamansu don ficewa daga yankin. A cewar dakarun dai wannan wata damace da zai ba su ikon nausawa yankunan da ke hannun 'yan tawayen sama da shekaru hudu.

Sai dai zafin hare-hare da ya raba birnin Aleppo gida biyu ya tilasta wa fararen hula sama 10,000 yin gudun hijira zuwa gabashin birnin. Masu ayyukan sa ido a Syriya dai na ganin cewa wannan sumame da dakarun ke kai wa shi ne irinsa mafi muni da 'yan tawayen suka fuskanta tun lokacin da suka mamaye birnin a shekara ta 2012.