Sojojin Sudan sun ƙaddamar da hari a yankin Darfur | Labarai | DW | 21.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Sudan sun ƙaddamar da hari a yankin Darfur

Dakarun gwamnatin ƙasar Sudan, sun ƙaddamar da babban hari ga matsugunin yan gudun hijira na Kalma dake yankin Darfur.

Rahotani daga yankin, sun bayyana cewar gwamnati ta abkawa wannan matsuguni a sakamakon zargin da ta ke masa, na kasancewa maɓuyar yan tawayen da su ka kaiwa yan sanda hari, a makon da ya gabata.

A ƙalla mutane dubu 90 ke zaune a matsugunin yan gudun hijirar Kalma.

A cewar kakakin matsugunin Abu Sharrad, kimanin sojoji dubu 2 na gwamnati, su ka yi wa yankin durra mikiya da sanhin sahiyar yau.

Ya zuwa yanzu babu addadin mutanen da su ka rasa rayuka, ko kuma su ka ji raunuka.

Sanarwar Gwamnatin Khartum ta ce sojoji sun kai wannan hari, da zumar maido doka da oda a matsugunin yan gudun hijira na Kalma.