Sojojin sa kai na Islama sun kwace garin Jowhar a Somalia | Labarai | DW | 14.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin sa kai na Islama sun kwace garin Jowhar a Somalia

Wasu madugan yaki su hudu a kasar Somalia sun tsere daga wani yanki na karshe dake hannunsu, bayan da sojojin sa kai na ´yan Islama suka kutsa cikin garin Jowhar. Rahotanni daga Mogadishu sun ce daga cikin hauloli akwai tsofaffin ministoci biyu na gwamnatin rikon karyar Somalia. Rohatannin sun ci-gaba da cewa ´yan Islama sun fatattaki abokan gabar su bayan wata ´yar gajeriyar musayar wuta. A kuma halin da ake ciki tsohon shugaban ´yan sandan Somalia Abdi Hassan Awale ya fice daga kawance haulolin yakin. Awale ya ce ya dauki wannan mataki sakamakon matsin lamba da ya sha daga shugaban kabilar su. Rahotannin baya bayan nan sun ce an halaka akalla mutane 19 a gumurzun da aka yi a garin na Jowhar.