Sojojin sa kai na Falasdinawa sun fara janyewa da tsakiyar Gaza | Labarai | DW | 20.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin sa kai na Falasdinawa sun fara janyewa da tsakiyar Gaza

Dakarun tsaron Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna sun fara janyewa daga wasu yankuna na birnin Gaza tare da sako mutanen da suka yi garkuwa da su, a karkashin wani sabon shirin tsagaita wuta. To sai dai duk da shirimn tsagaita wutar, a yau labaraba an kashe wasu ´ya´yan kungiyar Fatah guda biyu a wani sabon fada da aka gwabza tsakanin Fatah din da kuma sojojin sa kai na babbar abokiyar gabarta Hamas. Kungiyoyin biyu sun amince su janye dukkan sojojin sa kai daga kan tituna kana kuma sun saki mutanen da aka yi garkuwa da su a kwanakin nan. FM Falasdinawa Isma´ila Haniya yayi kira da a hada kai tsakanin al´umarsa bayan an halaka mutum 6 sakamakon gumurzun da aka yi a birnin Gaza. Shi ma a nasa bangare shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya sake yin kira da a kawo karshen mummunan fadan da ake yi a Zirin Gaza.