Sojojin sa kai a Nijeriya sun lashi takobin tsananta kai hare hare | Labarai | DW | 04.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin sa kai a Nijeriya sun lashi takobin tsananta kai hare hare

A cikin wani saƙon email da ta aika yau juma´a babbar ƙungiyar sojojin sa kai a Tarayyar Nijeriya ta sha alwashin tsananta gwagwarmaya ta zubar da jini. Kungiyar ta yankin Niger Delta da ake kira MEND ta ce burinta shi ne ta gurgunta harkar fid da mai a Nijeriya gaba ɗaya. MEND na ikirarin cewa tana fafatukar nemawa al´umar yankin Niger Delta kasonsu na arzikin mai da ake haka a wannan yanki. Hare haren ƙungiyoyin sojojin sa kai a yankin ya janyo raguwar kashi 20 cikin 100 na yawan mai da Nijeriya ke haƙowa wanda haka ya haddasa tashin farashin mai a duniya. MEND ta faɗawa mazauna yankin da su guji wuraren bincike na sojoji da wuraren da motocin sojoji suke domin za a auna su a hare-haren da ƙungiyar zata kai.