Sojojin NATO sun kashe ´yan Taliban 60 a Afghanstan | Labarai | DW | 23.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin NATO sun kashe ´yan Taliban 60 a Afghanstan

Mayakan Taliban kimanin 80 aka kashe a wasu hare hare ta sama da kuma ta kasa da dakarun kungiyar tsaro ta NATO suka ka a kusa da kan iyakar Afghanistan da Pakistan dake kudu maso gabashin Afghanistan. Rahotanni sun ce an hango mayakan na Taliban ne na shirin kai wani hari. Da farko dai dakarun kawance na kasashen yamma sun halaka ´yan taliban 30 yayin da suke gudanar da bincike akan rahotannin dake cewa fararen hula 25 na daga cikin wadanda sojojin NATO din suka kashe. Ana dai zargin Taliban da amfani da faraen hula a matsayin garkuwar ´yan Adam.